Sabon cefanen da Manchester United ta yi, Bruno Fernandes kan fan miliyan 47, bai iya tabuka komai ba yayin da Wolves ta rike wa United din wuya a filin wasa na Old Trafford.

A wasan da ba a samu damarmaki ba sosai, Fernandes ya kai ‘yan hare-hare, inda ya tilasta wa mai tsaron raga Rui Patricio tare kwallayen, wanda har ma ya kusa saka wata a cikin ragarsa bayan wani shot da Fernandes din ya buga.

Har sai a mintin karshe ne United ta samu kwallo mafi hadari, yayin da Diogo Dalot ya saka wa kwallon da Wan-Bissaka ya bugo kai zuwa gefen raga.

Tawagar ta Ole Gunnar Solskjaer maki hudu kacal ta samu daga wasa biyar da ta buga na baya-bayan nan.

Wolves ta yi bakin kokarinta amma duk da sako nata sabon cefanen na Daniel Podence ba ta iya amfana da kowacce dama ba a gaban raga.

Man United tana saman Wolves a mataki na shida da kuma na bakwai, kowaccensu da maki 35.

Idan Tottenham ta ci wasanta a gobe Lahadi tsakaninta da Manchester City, za ta haye samansu duka da maki 37.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *