Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga ‘yan Najeriya a daren yau Lahadi.

Sakataren watsa labarai na shugaban Femi Adesina ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook inda ya bayyana cewa shugaban zai yi jawabin ne ta gidajen talabijin da rediyo na kasar wato NTA da kuma FRCN, kuma ana sa ran sauran gidajen talabijin da rediyo za su yada jawabin shugaban kai-tsaye.

Shugaban dai zai yi jawabin ne da misalin karfe 7:00 na dare agogon Najeriya.

Duk da cewa Mista Femi Adesina bai bayyana mau’du’in da shugaban kasar zai tattauna a kai ba, amma ana ganin cewa shugaban zai fi mayar da hankali ne kan batun cutar coronavirus wadda ta zama annoba a fadin duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *