Shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya Malam Abba Kyari ya rasu bayan ya sha fama da jinya sakamakon kamuwa da cutar korona.

Mai magana da yawun Shugaba Buhari Femi Adesina ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a da misalin 12.50 na tsakar daren, a shafinsa na Twitter.

Abba Kyari ya rasu ne a Legas inda ya koma can bayan kamuwarsa da cutar korona ya ci gaba da jinya.

Dama rahotanni sun ce Abba Kyari yana fama da wata rashin lafiya kafin ya kamu da cutar korona, kuma masana harkar lafiya sun ce masu fama da wata cutar na daga cikin wadanda suka fi fuskantar hadarin mutuwa daga cutar ta korona.Hoton Hakkin Mallaka @FemAdesina@FEMADESINA

Sanarwar fadar shugaban kasar ta ce za a sanar da lokacin jana’izarsa nan gaba kadan.

A ranar 24 ga watan Maris ne aka tabbatar da cewa shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriyar ya kamu da cutar korona bayan komawarsa kasar daga Jamus.

Labarin ya ja hankalin ‘yan kasar sosai saboda girman mukaminsa.

Abba Kyari shi ne babban jami’in gwamnatin kasar na farko da ya harbu da covid-19.

A ranar 29 ga watan Maris ne abba Kyari ya rubuta wata budaddiyar wasika inda yake cewa ya tafi Legas domi ci gaba da jinya a kashin kansa, don ya dauke wa gwamnati nauyin kula da shi.

Tuni aka kirkiri wani maudu’i mai sunan Abba Kyari a shafin Twitter inda ‘yan Najeriya ke ta jajantawa tare da mika sakon ta’aziyarsu kan mutuwar ta sa.

Cikin dan kankanin lokaci an yi amfani da maudu’in sau dubun dubata.

Abba Kyari a takaice

Abba Kyari ya kasance mutum mai karfin fada a ji a gwamnatin Shugaba Buhari. 

Dan asali jihar Borno ne da ke arewa maso gabashin kasar. Kyari tsohon dan jarida ne, kuma tsohon ma’aikacin banki, inda ya rike manya-manyan mukamai a wasu bankunan kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *