“Bisa shawarar da Ma’aikatar Lafiya da hukumar NCDC suka bayar, na yi umarni da a dakatar da duk wata zirga-zirga a Jihar Legas da Abuja na tsawon mako biyu da zai fara daga 11:00 na daren Litinin 30 ga watan Maris.

“Wannan hanin zai hada da Jihar Ogun saboda kusancin da take da shi da Jihar Legas da kuma yawan zirga-zirga tsakanin jihohin. An sanar da gwamnonin Legas da Ogun da kuma ministan Abuja. 

“Lallai ne kowa ya kasance a cikin gidansa a wadannan yankunan. A katse tafiye-tafiye tsakanin jihohi. Dukkanin harkokin kasuwanci za a rufe su a tsawon wannan lokaci.

“Za mu yi amfani da wannan dama wajen gano tare da killace dukkan wadanda suka yi mu’amala da mutanen da aka riga aka gano sun kamu da cutar. Za mu tabbatar da cewa an kula da wadanda suka kamu a asibiti yayin da za mu takaita yaduwarta zuwa sauran jihohi.

“Wannan dokar ba ta shafi asibitoci da sauran cibiyoyin lafiya ba da kuma wuraren da ake samar da rarraba magunguna.

Haka nan ba ta shafi wuraren kasuwanci ba kamar su:a. Wajen sarrafa abinci da kamfanonin da ake sari;b. Wuraren da ake rarraba man fetur da masu sayarwa,c. Kamfanonin rarrabawa da samar da wutar lantarki;d. Kazalika ban da kamfanonin tsaro masu zaman kansuDuk da cewa dokar ba ta shafi wadannan wurare ba, to za a takaita ziyarrtarsu kuma za a sa ido.

“A yaki da coronavirus, kowanne irin mataki muka dauka ba zai yi girma ba kuma ba zai yi kadan ba. Maganar kawai ita ce ta daukar matakin da ya dace a lokacin da ya dace daga kwararrun ma’aikata.”

“Don Haka, a matsayinmu na gwamnati, za mu ci gaba da dogara da shawarwarin masana da kwararru a ma’aikatar Lafiya da hukumar da ke kula da yaduwar cutuka, NCDC, da sauran hukumomi a wannan lokaci na tsaka mai wuya.

“Ina kira ga duka ‘yan kasar nan da su bi dokokin da ake fitarwa lokaci zuwa lokaci. 

“Kamar yadda aka sani, Legas da Abuja ne garuruwan da ke da mafi yawan mutnen da aka samu dauke da cutar a Najeriya. Don haka mun mayar da hankali wajen gaggauta dakatar da yaduwar cutar, kuma mu taimaka wa sauran jihohin da yankuna iya karfinmu.

“Kawo yanzu, a Legas da Abuja, mun dauki daruruwan ma’aikata na wucin gadi don kara karfin cibiyoyinmu na amsa waya da kuma tallafa wa kokarinmu na gano mutanen da ake tunanin suna dauke da cutar da kuma wadanda aka yi wa gwaji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *