Kukan kwari masu harbi ko wadanda a karshe suke fadawa cikin abinci, na da ban takaici.

Sai dai, ya kamata mu nutsu, mu yi tunani sosai kafin amfani da abun kashe kwari, saboda yawan kwari a fadin duniya na raguwa sosai.

Kwari na taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci da kuma adana muhallinmu da dangoginsa.

“Idan muka dauke dukkannin kwarin da ke duniyar nan, mu ma za mu mutu,” kamar yadda Dakta Erica McAlister, babbar mai kula da gidan tarihin London na ”Natural History Museum,” ta shaida wa shirin BBC na “Crowd Science Programme”.

“Zamu mutu”

Ciye-ciyen da kwari keyi na taimakawa wajen saurin ragargaza abu ko kuma rubar da shi. Hakan kuma, na taimaka wa wajen samar da taki da ke karawa kasa inganci.

A dung beetle (Scarabaeus Satyrus) crawls over a ball of mud
Image captionKwari na taimakawa wajen gyara muhalli

“Ku tuna da za a ce ba mu da kwarin da za su cinye bahaya idan an yi….. abin da bai yi kyau ba. Idan babu kwari, da yanzu muna iyo cikin bahaya da rubabbun matattun dabbobi” in ji Dakat McAlister.

Suna kuma samar da abinci ga tsuntsaye da jemagu da kuma wasu kananan dabbobi.

“Kimanin kashi 60% na dabbobi masu kashin baya na dogaro da kwari ne don yin rayuwarsu, da dama daga cikin nau’ukan tsuntsaye da jemagu da kwadi da kuma kifin ruwa su ma suna bacewa”, in ji Dakta Francisco Sanchez-Bayo na Jami’ar Sydney.

A bee on a white flower
Image captionWani bincike ya bayyana cewa mutane na amfana da ayyukan da kwari wanda yawan sa ya kai dala biliyan 350

“Ya fada wa BBC cewa, “sake juya abubuwa masu amfani na gina jiki dungurungun din su na dogaro ne kan abubuwan da miliyoyin kwari ke aikatawa a karkashin kasa da kuma cikin ruwan da ba teku ba”.

Taimako a kyauta

Bugu da kari ba cin samar da abinci da suke yi wa sauran na’ukan dabbobi da kuma raya muhalli da dangoginsa ta hanyar sake inganta shi, kwari na gudanar da wani muhimmin aiki kuma – samar da ababen raya furanni, wanda muhimmin abu ne na samar da abinci.

Wani bincike da aka gudanar ya kiyasta cewa, mu mutane muna amfana da ayyukan da kwari ke gudanarwa wanda yawan sa ya kai dala biliyan 350.

A bee on a white flower
Image captionWani bincike ya bayyana cewa mutane na amfana da ayyukan da kwari wanda yawan sa ya kai dala biliyan 350

Har yanzu kuma ba mu cika mai da hankali kan taimakon da muke samu daga wadannan kwari ba.

“Akwai kimanin kwari 17 da ke gina cakuleti. 15 daga ciki suna cizo wanda kowa ba ya so. Daya dan karamin cinnaka ne, dayan kuma wani dan mitsitsin kwaro ne. Sai dai ba mu san wani abu mai yawa game d asu ba”, in ji dakta McAlister.

Abun da muka sani shi ne, yawan kwarin nan a kasashe da dama na raguwa kamar su kudan zuma.

Wasu sanannun nau’ukan malam bude littafi wanda ke samar wa furanni da dama ababen sa su girma na raguwa.

Sai dai abin tambaya shi ne muna cikin hadarin matsalar kawar da su har sai lokaci ya kure mana, yayin da muke cin karo da kwarin ko da yaushe?

Yawan su

Duniyar kwari ta yi wa yawancinmu girma mu fahimce ta. A cewar Makarantar Smithsonia ta Amurka, baki daya nauyin kwarin da ke duniya ya fi na mutane sau 17.

A man tries to catch locusts while standing on a rooftop as they swarm over the Yemeni capital Sanaa
Image captionKwari na haddasa wa mutane matsaloli da dama

Makarantar ta kiyasta cewa, a lokaci daya, za a iya samun kwari biliyan sau biliyan a doron kasa.

Masu kula da muhalli dai har yanzu ba su amince kan nau’ukan kwari nawa ake da su ba – daga dai miliyan biyu zuwa 30.

Amma ba kamar manyan dabbobi ba, ba a cika samun bincike mai tsawo a kan kwari ba.

A cewar Makarantar Smithsonia, mun san kawai kimanin ire-iren kwari guda dubu dari tara 900,000. Amma wannan adadin ma na wakiltar kimanin kashi 80% cikin dari na nau’ukan kwarin da ke duniya ne kawai

Gushewa a doron kasa

Sai dai duk da yawansu babu wata kariya da suke samu daga hana su gushewa a doron kasa.

A worker picks coffee cherries from a coffee plant
Image captionMasana kimiyya sun ce abu kadan suka sani game da kwarin da ke da alfanu a gare mu kamar wadanda ke lalata gahawa

Kwari na mutuwa wasun su tun ma kafin a gano su a rarrabe su.

Dr McAlister ta ce “Muna da misalan hakan da muka samu a shekarun 1930 da 1940 wadanda har yau ba a gano su ba. Sai dai tuni aka kawar da su daga doron kasa.

Hasashe mara dadi

A Wani rahoto da aka wallafa a wata Mujallar Biological Conservation a watan Fabrairun 2019 ya yi wani hasashe mara dadi.

A black crow eating an insect
Image captionTsuntsaye da dabbobi suna cin kwari a matsayin abincinsu

Rahoton ya ce yawan kwari a Jamus da Birtaniya da kuma Puerto Rico – wato kasashe uku da ake ta nakaltar al’amarin kwari cikin shekara 30 da suka gabata – yawan kwari kasashen na raguwa da kashi 2.5 cikin 100 duk shekara.

Raguwar na sanya damuwa

A Wani bincike da aka yi a shekarar 2017 ya nuna cewa kwari masu tashi sun ragu da fiye da kashi 75 cikin 100 a fiye da kusan shekara 30 a wurare 60 da ake karewa a Jamus.

A honey bee gathering nectar from a purple flower
Image captionA kasashe da dama, yawan kudan zuma na raguwa

A tsibirin Caribbean na Puerto Rico, wani malami a Amurka ya gano raguwar kashi 98 cikin dari na adadin kwari cikin shekara 40.

Da wannan, yawancin nau’in na iya bacewa.

Masu kisa

Rashin samun mazauni sakamakon ayyukan gona na daga cikin manyan dalilan da suke korar kwari – kamar kwarin da ke lalata bishiyoyi har su gushe daga ban kasa.

Edible insects and bugs seen for in Nanning, Guangxi Region, China.
Image captionWasu na ganin kwari kamar za su maye gurbin nama

“Wadannan kwarin suna bukatar bishiyoyi domin biyan bukatunsu. Za a rasa bishiyoyin da ke ba da inuwa – wadanda manyan kwari ke bukata sannan sun rasa mazaunin da suke bukata,” in ji Dr McAlister.

Yawan yin amfani da magungunan kwari da dumamar yanayi su ma suna ba da gudummawa wajen raguwar kwarin.

Kyankyasai

Labari mara dadi shi ne kwari kamar kyankyasai na iya lalata tsarin saboda akwai alamun sun samu kariya daga magungunan kwarin.

Cockroaches locked in a container for research
Image captionDumamar yanayi zai haddasa karuwar kwari kamar kyankyasai

“Kwarin da ke saurin kyankyasa za su fi cin kasuwa saboda yanayi na dumi, saboda akasarin saboda da yawa daga cikin abubuwan da suke gaba dasu, wadanda ke daukan lokaci kafin su hayayyafa, za su gushe,” kamar yadda Farfesa Dave Goulson na Jami’ar Sussex ya shaida wa BBC.

“Abu ne mai yiwuwa a ce za mu iya kawo karshen annobar wasu nau’in kwari, amma za mu rasa duk kyawawan kwarin da muke so, kamar kudan zuma da malam buda mana littafi.”

Ceton kwari

Amma masana kimiyya na cewa akwai sauran lokaci na daukar matakan gyara.

Francisco Sanchez-Bayo ya ce “wannan ya hada da dasa bishiyoyi da tsirrai da furanni a filaye da kawar da magungunan kashe kwari masu hatsari daga kasuwa, da aiwatar da ingantattun tsare-tsaren manufofin rage iskar carbon”.

Ya ce shawarar da mutane suka yanke kamar komawa cin abinci na gargajiya su na iya taimakawa wajen kawo sauyi ga kwarin duniya.

“Hakan zai karfafa wa manoma su rage yawan magungunan kashe kwari da suke amfani da su a gonakinsu, zai kuma taimaka wajen rage abubuwa masu guba da ke cikin muhalli.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *