0 Comments

A karon farko an samu wanda ya mutu bayan kamuwa da cutar covid-19 a Jamhuriyar Nijar.

Kazalika an kuma samu karin mutum hudu da suka kamu da cutar abin da ya kawo adadinsu ya zuwa yanzu bakwai a kasar.

A makon daya gabata ne Nijar din ta shiga jerin kasashen duniya da aka samu bullar coronavirus.

Mutumin farko da ya kamu da cutar dai dan kasar ne mai shekara 36 wanda ke aiki a a wani kamfanin zirga-zirgar motoci, bayan ya fito daga Lome, ya je Ghana ya je Burkina Faso, sannan ya koma kasarsa.

Bayan ‘yan kwanaki kadan da gano alamomin wannan ciwon, a lokacin ne aka shiga yi masa bincike sannan da aka gano yana da cutar (don haka) sai aka kwantar da shi.

Bayan kwanaki kadan ne a tsakani aka sake samun mutum na biyu da ya kamu cutar a kasar.

Mutumin dai dan kasar Italiya ne da ke aiki da wata kungiya mai zaman kanta a kasar.

Hukumomi a kasar sun ce mutumin ya shiga kasar ne tun a ranar 28 ga watan Fabrairun da ya gabata amma bai nuna alamar cutar ba sai a ranar Asabar.

Wannan layi ne

Tuni dai kafin bullar cutar a kasar, gwamnatin kasar ta dauki matakai na kariya da hana yaduwarta.

Daga cikin matakan an soke tarukan sallar juma’a da sauran sallolin jam’i, haka su ma jagororin addinin kirista sun bukaci mabiyansu su dakatar da tarukan ibada a coci-coci musamman ma dai na karshen mako.

Kazalika an bayar da umarnin duk ya zo a killace shi idan ya fito daga inda ake fama da cutar, ko ba ka hadu da ciwon ba ana killace mutum na kwana 14, wanda ya fito hanyar kasa ma ana killace shi.

Ya zuwa yanzu dai akwai adadin mutum fiye da dubu daya da dari shida da suka kamu da coronavirus a nahiyar.

Tuni dai kasashen nahiyar suka dauki matakai daban-daban na kariya da kuma hana yaduwar cutar a kasashen su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *