Wata matar aure, mai suna Rabi’atu Musa, mai shekaru 28 ta gamu da ajalinta a sanadin wata gobara da sanyin safiyar Laraban nan, a unguwar Gayawa da ke yankin karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bakin mai magana da yawunta, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ta tabbatar da afkuwar lamarin.

Wasu bayanai da BBC ta samu na zargin cewa, matar ce ta cinna wa kanta wuta, bayan da ta kai ‘ya’yanta su shida wani daki daban ta ajiye su, lokacin da mai dakinta ya fita sallar asuba.

Kokarin da wakilin BBC ya yi don jin ta bakin mijin marigayiyar ya ci tura.

Sai dai wasu mazaunan unguwar ta Gayawa sun shaida wa BBC, cewa babu wanda ya san takamaiman abin da ya kai matar kashe kanta.

Wani makwabcin gidan da marigayiyar take, mai suna Sulaiman, ya ce ya yi aune da aukuwar lamarin ne da safe, yayin da ya fito zai tafi wajen wani taron sadakar uku, ya tambaya aka ce masa wata baiwar Allah ce ta kone a gidan.

”Mutane wasu za ka ji suna ta surutu, suna cewa ita ta kona kanta a kan kishi, a kan me ye, to Allah Shi ne masani a kan wadannan al’amuran.

Ba ka da shaidar da za ka tabbatar cewa ita ce ta kashe kanta, ko ba ita ba ce ba”.

Ita kuwa wata makwabciyar wadda ba ta bayyana sunanta ba, ta bayar da shaida cewa, marigayiya Rabi’atu Musa dai ba ta da matsala da makwabta kafin rasuwarta,

”Amma dai gaskiya tana da kishiya, wadda a da gida daya suke amma daga baya an raba masu gida”.

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano dai ta tabbatar da labarin aukuwar lamarin, inda mai magana da yawun rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana wa BBC cewa, sun tarar da matar ta kone.

Ya kara da cewa su ne suka dauke ta cikin gaggawa, suka kai ta babban asibitin Murtala da ke cikin birnin Kano, inda likita ya tabbatar masu cewa matar ta rasu.

Daga nan suka mika gawarta ga ‘yan uwanta domin yi mata sutura.

Dangane da zargin da ake yi cewa, matar ita ce ta kashe kanta, sai mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ya ce, ”Yanzu haka dai mun dukufa kan bincike, hakazalika kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Abu A Sani ya ba da umarni a gudanar da bincike a kan faruwar wannan lamari”.

Idan ba a manta ba dai, ko a kwanakin baya sai da aka sami aukuwar wata gobara a wani gida da ke kusa da gidan da Rabi’atu Musa da mijinta ke zaune, inda wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba, suka kona wani magidanci da iyalinsa ta hanyar sa masu wuta, bayan da aka garkame kofar shiga dakinsu da kwado daga waje, wutar kuma ta halaka su baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *