Manchester United ta amince ta dauki dan wasan tawagar kwallon kafa ta Portugal, Bruno Fernandes daga Sporting Lisborn.

United za ta biya fam miliyan 47, kudin dan wasan mai shekara 25, sannan da akwai karin tsarabe-tsarabe da nan gaba zai kai fam miliyan 67.6.

Yanzu abin da ya rage shi ne auna lafiyar dan kwallon, sannan ya saka hannu kan kwantiragi

www.hausaplus.com

Tun da aka bude kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallon Turai, United ta dunga zawarcin Fernandes.

Sai a ranar Talata ne United ta cimma matsaya da Sporting Lisbon, bayan da Barcelona ma ke son sayen dan wasan.

Fernandes ya koma wasa Sporting Lisbon daga Sampdoria kan fam miliyan 7.2 a shekarar 2017.

Dan wasan ya ci kwallo 64 a wasa 137 a dukkan fafatawar da ya yi, ya kuma lashe kofin gasar Portugal a 2018/19.

Fernandes shi ne ya lashe kyautar dan wasan da babu kamarsa a gasar Portugal a 2017/18 da kuma a 2018/19.

Ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Portugal wasa 19, yana cikin ‘yan kwallon da suka ci wa kasar UEFA Nations League.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *